Abahlali base Mjondolo

Abahlali base Mjondolo
Bayanai
Suna a hukumance
Abahlali baseMjondolo
Iri Tsarin Siyasa, harkar zamantakewa da tenants' union (en) Fassara
Ƙasa Afirka ta kudu
Laƙabi AbM
Aiki
Mamba na Poor People's Alliance (en) Fassara
Tarihi
Ƙirƙira 2005
abahlali.org

Abahlali baseMjondolo (AbM, furcin Zulu: [aɓaˈɬali ɓ disputasdʒɔˈndɔːlo], a cikin Turanci: "mazaunan shacks"). ƙungiya ce ta mazaunan shacks a Afirka ta Kudu wacce da farko ke kamfen don ƙasa, gidaje da mutunci, don dimokuradiyya al'umma daga ƙasa da kuma adawa da xenophobia.

Wannan yunkuri ya fito ne daga toshewar hanya da aka shirya daga ƙauyen Kennedy Road a birnin Durban a farkon shekara ta 2005 kuma tun daga lokacin ya fadada zuwa wasu sassan Afirka ta Kudu. Ya zuwa Oktoba 2022 ya yi iƙirarin cewa yana da mambobi sama da 115,000 a cikin rassa 81 a cikin larduna huɗu daga cikin tara na Afirka ta Kudu - KwaZulu-Natal, Mpumalanga, Gabashin Cape da Gauteng .

Fiye da ashirin daga cikin shugabannin ta an kashe su, wani abunda yasa akayi zargi a kan majalisa mai mulki na Afirka.[1][2]

Ercument Celik ya rubuta cewa "Na fiskanci irin yadda ƙungiyar ke gudanar da tarurrukanta ta hanyar dimokuradiyya".

A Wani labarin da aka yi a cikin The Times ya bayyana cewa yunkurin "ya girgiza yanayin siyasa na Afirka ta Kudu. Masanin kimiyya Peter Vale ya rubuta cewa Abahlali baseMjondolo "tare da Kamfen ɗin Ayyukan Magunguna shine mafi inganci a cikin al'ummar farar hula ta Afirka ta Kudu". Khadija Patel ta rubuta cewa yunkuri ne "a kan gaba na sabon guguwar siyasa".

Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.
  1. The bloody battle for land and rights in Cato Manor, Greg Arde & Benita Enoch, GroundUp, 11 October 2022
  2. More than twenty activists killed in eThekwini battle for land, Paddy Harper, Mail & Guardian, 13 October 2022

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Nelliwinne