Abdelbaki Hermassi ( Larabci: عبد الباقي الهرماسي ; haihuwa, ranar 26 ga Disamban shekarar 1937, a birnin Fériana, Tunisia zuwa mutuwarsa a 23 ga Oktoban shekarata 2021) ɗan siyasan Tunisiya ne. Ya kasance minitan harkokin kasashen waje ne na Tunisia tun lokacin da ake nada shi a ranar 10 Nuwamban 2004 lokacin da aka sake tsarin majalisa, har zuwa 17 ga watan Augustan 2005 lokacin da aka sake wani sabon tsarin kuma ya rasa kujerarsa.