An haifi Abdullah a ranar 30 ga watan Janairun shekara ta 1962 a asibitin Falasdinu a Al Abdali, Amman, ga Sarki Hussein da matarsa ta biyu ta Burtaniya, Gimbiya Muna Al-Hussein (an haife ta Toni Avril Gardiner). [1][2] Shi ne sunan kakan mahaifinsa, Abdullah I, wanda ya kafa Jordan na zamani.[3][4] Daular Abdullah, Hashemites, ta mallaki Makka sama da shekaru dari bakwan 700 - daga karni na goma 10 har zuwa lokacin da Gidan Saud ya ci Makka a shekara ta 1925 - kuma sun mallaki Jordan tun a shekarar 1921. [5] Hashemites sune daular da ta fi tsufa da dadewa aDuniyar Musulmi.[6] Bisa ga al'adar iyAli, Abdullah ita ce zuriyar ta arba’’in da daya 41 ta 'yar MuhammaduFatimah da mijinta, Ali, Khalifa Rashidun ta huɗu.[1][7]