Abeokuta Birni ne, da ke a jihar Ogun, a ƙasar Najeriya. Shi ne babban birnin jihar Ogun. Birnin na nan a kudancin rafin Ogun, a wani yanki dake da duwatsu da manyan itace na Savanna.[1] Birnin na da nisan kilomitoci 77 (48 mi) daga arewacin Legas ta titin jirgin kasa, ko kuma nisa 130km (81 mi) ta ruwa. Bisa ga ƙidayar jama'a a shekarar 2006, jimillar mutane 451,607 ne.
↑"Hoiberg, Dale H., ed. (2010). "Abeokuta". Encyclopædia Britannica. Vol. I: A-ak Bayes (15th ed.). Chicago, IL: Encyclopædia Britannica Inc. pp. 27. ISBN978-1-59339-837-8.