Abincin Tunisiya

Lablabi babban sopo ne da aka yi da chickpeas da tafarnuwa
Wurin Tunisia

Abincin kasar Tunisiya, Abincin Tunisiya, ya ƙunshi al'adun dafa abinci, sinadaran, girke-girke da dabarun da aka haɓaka a Tunisiya tun zamanin d ̄ a. Yafi haɗuwa da abincin Bahar Rum da na asalin Berber tare da tasirin Punic. A tarihi, abincin Tunisiya ya ga tasiri da musayar tare da al'adu da kasashe da yawa kamar Italiya, Andalusians, Faransanci da Larabawa.[1]

Kamar kasashe da yawa a cikin Bahar Rum, abincin Tunisiya ya dogara ne da Man zaitun, kayan yaji, Tumatir, abincin teku da nama. Duk da haka, yana da ɗanɗano na musamman wanda ya bambanta da abincin da ke kewaye da shi.

  1. Editorial Staff (2022-09-29). "Tunisian Cuisine — Mentality, Spirit & Character". Carthage Magazine (in Turanci). Retrieved 2023-10-19.

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Nelliwinne