Ahl al-Bayt

Ahl ul-Bayt
iyali
Bayanai
Suna a harshen gida أَهْلُ البَيْتِ da آلُ البَيْتِ
ahl al bayt

Ahlul Baiti ( Larabci: أَهْل ٱلْبَيْت‎ , lit. ' na nufin iyalan gidan Annabi Muhammad, amma kuma an faɗaɗa a mahangar Sunna don ya shafi dukkan zuriyar Banu Hashim (dangin Muhammad) har ma da dukkan musulmi.[1][2] A cikin addinin Shi'a, kalmar ta takaita ga Muhammadu; ƴarsa Fatima, da ɗan'uwsn sa kuma surukinsa Ali, da ƴaƴansu biyu, Hasan da Husaini. Ra'ayin Ahlus-Sunnah gama gari yana ƙarawa da matan Muhammadu akan waɗannan biyar.[3]

Yayin da dukkan musulmi ke girmama Ahlul-baiti, [4] [5] Shi'a ne ke da kima ga Ahlul Baiti ta hanyar ɗaukar su a matsayin shugabannin al'ummar musulmi. Shi'a ƴan Sha biyu kuma sun yi imani da ikon fansa na azaba da shahada da Ahlul Baiti suka sha, musamman na Husaini. [2] [4]

  1. Brunner 2014.
  2. 2.0 2.1 Campo 2009.
  3. Goldziher, Arendonk & Tritton 2022.
  4. 4.0 4.1 Campo 2004.
  5. Mavani 2013.

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Nelliwinne