Ahmadiyya | |
---|---|
| |
Bayanai | |
Iri | ma'aikata |
Ƙasa | Punjab (Indiya), British Raj (en) da Indiya |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1889 |
Wanda ya samar | |
alislam.org |
Ahmadiyya (Urdu احمدیہ Ahmadiyya) tafiyar imani ce ta addini wadda aka kafa ta a ƙarni na (19), Mirza Ghulam Ahmad ne wanda mabiyan sa suka haƙiƙance kan cewar shine Mahdi ya kafa tafiyar. An kafa tafiyar ne tun kafin Indiya ta rabu zuwa wannan Indiyar ta yanzu wato rabewar ta da Pakistan da Bangladesh.
Ahmad yaso ya sabunta Musulunci, tare da da'awar dawo da ainahin koyarwa ta addinin Musulunci.a shekara ta alif( 1914), tafiyar ta rabe zuwa gida biyu, a sakamakon wanda zai zamo magajin Ahmad kuma har yanzu waɗannan ɓangarorin sunanan. Mirza Ghulam Ahmad yayi da'awar cewa ya cika annabatar Mahdi. Ana yi masa laƙani da Mujaddadi na ƙarni na( 14), kuma Yesun da aka alkawarta zuwan sa.[1][2][3][4][5]
Yan Ahmadiyya na ɗaukar kansu a matsayin Musulmai kuma suna da'awar sunayin addinin Musulunci ne wanda Annabi Muhammad ya koyar. Mirza Ghulam Ahmad ya kafa tafiyar ne a shekara ta alif(1889 ), kuma ya saka mata suna Ahmadiyya Muslim Jamaat Fatan sa shine ya dawo da ruhin Musulunci. .
Ainahin tafiyar Ahmadiyya ya tsage zuwa gidaje biyu[6] bayan rasuwar Nooruddin,magajin Ghulam Ahmad na farko.
Waɗannan tafiyoyin biyu sune Jama'ar Ahmadiyya da kuma Jama'ar Ahmadiyya ta Lahore (Ahmadiyya Anjuman Ishaat-i-Islam, AAIIL). Ɓangarorin nada bambanci ga hanyar koyarwa a tsakanin su.[6][7]
Babban ɓangare na Jama'ar Ahmadiyya na da rassa a sama da ƙasashen duniya (190), babbar cibiyarta na a birnin Landan na Ingila. Karamin tsagin kuma da akafi sani da Jama'ar Ahmadiyya na Lahore nada cibiya a Lahore, kuma anfi sanin su a Jamani, Autraliya da Pakistan.
Abinda ke kawo rigima shine fahimtar Ahmadiyya dangane da rasuwa da dawowar Annabi Isah da kuma mahangar su ga Jihadi. Hakanan ma Yan Ahmadiyya Nada bambancin ta Ƙur'ani( 33:40. ), Wannan aya tana magana akan cewa Annabi Muhammad shine cikamakon Annabawa. Sai dai mabiya Jama'ar Ahmadiyya ta Lahore basu da taraddadi dangane da wannan batun domin su basu kallon Mirza Ghulam Ahmad matsayin Annabi. A wannan dalilin ne yasa sukafi kusanci da aƙidar Musulunci.
Yan Ahmadiyya sun fassara ƙur'ani da dukkannin manyan harsunan duniya. Kuma suna yada aƙidun su da da'awar su awa (24), a tashoshin su na talabijin din su waɗanda suka haɗa da, MTA 1,MTA 2, MTA 3 (domin Larabawa masu kallo) kuma kwanannan suka ƙaddamar da sabuwar tashar MTA Africa. Yan Ahmadiyya na samar da malamai, likituci,masu kare yancin Dan Adam a ƙasashen da suka cigaba.