![]() | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Bayanan tarihi | ||||
Ƙirƙira | 1620s | |||
Rushewa | 1734 |
Akwamu (ana kuma kiran sa Akuambo) jiha ce da mutanen Akwamu suka kafa a cikin ƙasar Ghana ta yanzu. Babban birnin Masarautar Akwamu ana kiransa Akwamufie. Bayan yin ƙaura daga jihar Bono, Akan waɗanda suka kafa Akwamu suka zauna a Twifo-Heman. Akwamu ya jagoranci daular faɗaɗa a ƙarni na 17 da 18. A lokacin daular su, Akwamu sun kirkiro al'adu masu tasiri wadanda suka ba da gudummawa ga Ghana.