Alaafin Oyo & Sir Walter Egerton circa 1910 - Colorized Kofar kofar fadar Alaafin Oyo mai suna "Oju Abata"
Alaafin, ko kuma mai kula da fada a yaren Yarbawa, shi ne sarautar sarkindaular Oyo ta tsakiya[1] da kuma garin Oyo na yammacin Afirka a yau. Take ko Suna ne, na musamman na Oba (sarkin) na Oyo.[2] Wani lokaci ana fassara kalmar a matsayin “sarki”. Sarkin Oyo ya mulki tsohuwar daular Oyo, wadda ta taso daga jamhuriyar Benin ta yau zuwa Najeriya, wadda ta samo asali daga jihohin Kudu maso Gabas da Yamma zuwa Arewa. Mutanen da ke ƙarƙashinsa ana kiransu Yarabawa kuma suna magana da harshen Yarbanci.