Amadou Sanogo | |||
---|---|---|---|
22 ga Maris, 2012 - 12 ga Afirilu, 2012 ← Amadou Toumani Touré - Dioncounda Traoré (mul) → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Ségou, 30 Nuwamba, 1972 (52 shekaru) | ||
ƙasa | Mali | ||
Karatu | |||
Harsuna | Faransanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da soja | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | independent politician (en) |
Amadou Haya Sanogo (an haife shi a shekara ta 1972 ko kuma a shekara ta 1973)[1] hafsan sojan Mali ne wanda ya jagoranci juyin mulkin Malin a 2012 akan shugaba Amadou Toumani Touré . Ya ayyana kansa a matsayin shugaban kwamitin farfado da dimokuradiyya da dawo da jihar (CNRDRE).[2] An kuma ce Sanogo yana da hannu wajen kamawa da murabus din mukaddashin Firayim Minista Cheick Modibo Diarra a watan Disamban shekarar 2012, wanda kuma ya kai ga naɗa ma'aikacin gwamnati Django Sissoko a matsayin Firayim Minista. A cewar Human Rights Watch, sojojin Sanogo suna da hannu a cikin munanan take hakkin dan Adam da suka hada da azabtarwa, cin zarafi, da kuma tsoratarwa ga 'yan jarida da dangin sojojin da aka tsare. [3]