Amanda Anne Milling (an Haife ta 12 ha watan Maris 1975) Yar siyasa ce Biritaniya wacce ke aiki a matsayin Ministar Kasa ta Asiya da Gabas ta Tsakiya tun 2021 kuma memba ce a Majalisar (MP) na Cannock Chase tun babban zaben 2015 . Ta yi aiki a matsayin Minista ba tare da Fayil ba a cikin majalisar ministocin Burtaniya kuma, tare da Ben Elliot, a matsayin Mataimakin Shugaban Jam'iyyar Conservative daga Fabrairu 2020 zuwa Satumba 2021. Ta taba yin aiki a binciken kasuwa.