![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
zone of Ethiopia (en) ![]() | |||||
Bayanai | |||||
Ƙasa | Habasha | ||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Habasha | ||||
Region of Ethiopia (en) ![]() | Afar Region (en) ![]() |
Awsi Rasu, Wanda kuma aka fi sani da shiyya ta 1 ta Gudanarwa, shiyya ce a yankin Afar na kasar Habasha . Wannan shiyyar tana iyaka da kudu da Gabi Rasu, a kudu maso yamma da Hari Rasu, a yamma da yankin Amhara, a arewa maso yamma da Fantí Rasu, a arewa ta yi iyaka da Kilbet Rasu, a arewa maso gabas da Eritriya, daga gabas kuma tana iyaka da ita . da Djibouti .
Garin mafi girma a cikin Awsi Rasu shine Asayita . Kogunan da ke wannan shiyyar sun hada da na Awash da magudanan ruwa na Mille da Logiya . Akwai tafkuna guda shida masu alaka da juna a wannan Shiyya, wadanda Awash ke ciyar da su: daga arewa zuwa kudu sune Gargori, Laitali, Gummare, Bario da Tafkin Abbe (ko Abhe Bad).