Baha'i

Baha'i
Founded unknown value
Mai kafa gindi Bahá'u'lláh
Classification
Alamar Addinin Baha'i
Addinin Baha`i
gurin bautan mabiya Addinin BAHA`I

Baha'i,wani addini ne da ya fara a shekara ta 1800 daga wani mutum dan ƙasar Iran wanda ake kira Bahá'u'lláh wanda aka haifa a birnin Tehran na ƙasar ta Iran. Mabiya addinin Baha'i sunyi imani da Bahá'u'lláh a matsayin annabin Allah ne kuma yana koya wa mutane sanin Ubangiji da bauta masa.

Akidar mabiya Baha'i sun yarda da Ubangiji daya. Sun yarda Bahá'u'lláh yana dauko sakon Ubangiji zuwa ga halitta. Bahá'u'lláh yace bashine na farko ba wajen kawo sakon Ubangiji kuma bashi ne na karshe ba, yace shima kamar sauran Annabawa yake kamar Yesu, Muhammad, Ibrahim da Musa,sanann kuma shima kamar sauran jagiririn addinai yake irin su Krishna da Buddah. Yace yana kallon dukkannin su a matsayin Manzannin Ubangiji ne. An kuma haifi Bahá'u'lláh a gidan Musulmai ne kafin ya kafa nasa addinin mai kama da Musulunci. Mabiya Baha'i sun hakikance da babu wani Annabi bayan Bahá'u'lláh sai an samu shekaru 1000 bayan rasuwar sa.


From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Nelliwinne