| |
Iri | rikici |
---|---|
Bangare na | War in Afghanistan (2001–2021) (en) |
Kwanan watan | 27 Nuwamba, 2008 |
Wuri | Badghis Province (en) |
Balamorghab wani harin kwantan ɓauna ne daya faru ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar 2008, lokacin da wasu 'yan ta'addar Taliban karkashin jagorancin Ghulam Dastagir suka kai wa motocin dake dauke da jami'an tsaron Afghanistan hari. An kai harin kwantan bauna a kusa da Balamorghab da ke lardin Badghis a arewa maso yammacin Afganistan, kuma ya yi sanadin salwantar da rayukan dakarun gwamnati. An bayyana shi a matsayin daya daga cikin hare-haren wulakanci da jami'an tsaron Afghanistan suka taba fuskanta.