![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Haihuwa | jahar Kano, 1959 (65/66 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Ƴan uwa | |
Ahali | Murtala Mohammed |
Karatu | |
Harsuna |
Hausa Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | marubuci |
Balaraba Ramat Yakubu kwarariyar marubuciyar littattafan Hausa ce da ake wa laƙabi littattafan soyayya. An haife ta a cikin birnin Kano a a shekara ta alif ɗari tara da hamsin da tara 1959A.c[1] . Tana daga kalilan marubuta da aka fassara littafinta zuwa harshen Inglishi. Rubuce - rubucenta sun fi bada muhimmanci akan zamantakewar aure da kuma gwagwarmayar mata a rayuwar Hausawa, musamman tauye hakkin mata da mazan Hausawa kan yi, zamu ga haka a littattafan ta kamar Budurwar zuciya da mashahurin littafin ta Alhaki kuikuyo ne.