Birnin Kebbi, birni ne wanda yake a yankin Arewa Maso Yammacin Najeriya. Shine cibiyar Jahar Kebbi kuma shine mazaunin Masarautar Gwandu. A kidayar shekara ta 2007 akwai yawan jama'a a birnin kimanin 125,594.
Kebbi mafiya yawan mutanen jahar Hausawa ne da Fulani kuma Musulunci ne addinin da kuma yafi rinjaya a birnin.
Birnin Kebbi ne mazaunin fadar Masarautar Kebbi a da, wadda daga baya ta koma garin Argungu bayan bude ta da Gwandu ya yi a shekara ta 1831.[1]
- ↑ https://www.britannica.com/place/Birnin-Kebbi