Cry Freetown | |
---|---|
Asali | |
Lokacin bugawa | 2000 |
Asalin suna | Cry Freetown |
Asalin harshe | Turanci |
Ƙasar asali | Saliyo |
Characteristics | |
Genre (en) ![]() | documentary film |
Direction and screenplay | |
Darekta |
Sorious Samura Ron McCullagh (en) ![]() |
Kintato | |
Narrative location (en) ![]() | Saliyo |
External links | |
Specialized websites
|
Cry Freetown fim ne na gaskiya da aka shirya shi a shekarar 2000 wanda Sorious Samura ya jagoranta. Labari ne na waɗanda yakin basasar Saliyo ya rutsa da su kuma yana nuna lokacin mafi muni da 'yan tawayen Juyin Juya Hali (RUF) suka kwace babban birnin ƙasar (Janairu 1999). Fim ɗin ya kuma nuna yadda sojojin Najeriya ke aiwatar da hukuncin kisa a takaice. An watsa shi a CNN International a ranar 3 ga watan Fabrairu, 2000. An shirya fim ɗin tare da taimakon CNN Productions, shirin labarai na Dutch 2Vandaag da Insight News Television. Kyaututtuka na fim ɗin daya samu sun haɗa da lambar yabo ta Emmy, lambar yabo ta BAFTA, lambar yabo ta Peabody da lambar yabo ta azurfa ta 2001 a Alfred I. duPont–Columbia Jami'ar Awards.[1]