Daular Kanem-Bornu | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Babban birni | Njimi | ||||
Yawan mutane | |||||
Harshen gwamnati | harsunan sahara | ||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Kanem Empire (en) | ||||
Ƙirƙira | 11 century | ||||
Rushewa | 22 ga Afirilu, 1900 |
Daular Kanem–Bornu ta kasance daula ce data taka kasancewa wurin da a inda ayau nan ne kasar Cadi da Nijeriya. Masanan kasashe larabawa suna kiran daular da Kanem Empire daga karni na 9th har zuwa sanda takasance daular musulunci Bornu (Daular Bornu) a Shekarar 1900. Kanem Empire CE tun daga shekara ta (c. 700 zuwa 1380) takasance ne kasashen Chad, Nigeria da Libya.[1] A matukar girmar daular ta tattara kasashe ba kawai daukacin kasar Chad ba, takai har zuwa kudancin kasar Libya (Fezzan) da gabashin Nijar, arewa maso gabas din Nigeria da arewacin kamerun. A yayin da Daular Bornu take a shekara ta (1380s zuwa 1893) takasance a inda ake kira ayau arewa maso gabashin Nigeria, wanda tacigaba da girma fiye da daular Kanem, ta tattari kasashen da ayau sune ko kuma suke daga cikin kasashe kamar Chad, Nijar, Sudan, da Cameroon; an samar da’ita daga shekara ta 1380s zuwa shekarar 1893. Farkon tarihin daular an santa ne da jerin masu sarautar ko Girgam matafiyin bincike dan kasar jamus wato Heinrich Barth wanda aka gano a shekarar 1851.