Daurama | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Hausa |
Mutuwa | Daura, |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Bayajidda |
Yare | Kabara |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ruler (en) |
Daurama ko Magajiya Daurama (ƙarni na 9) ta kasance mai mulkin mutanen Hausa wacce ita ce ta kasance Kabara ta ƙarshe a tarihin Daura. Ana ce mata Kabaran Daura. Masu bada labaran gargajiya suna tunata ne a matsayin Sarauniya ne, Uwa ta Daular Hausawa dake Arewacin Najeriya a yankin Nijar (kasa) da kuma Najeriya. Labarin Magajiya Daurama ana bayar da shi ne a labaran jarumtaka na jarumi Bayajidda.
Magajiya Daurama tayi mulki a garin da ake kira ko ake cewa Daura.
An saka wa garin sunanta, wanda yanzun Daura masarauta ce mai zaman kanta a Jihar Katsina, Najeriya. Tsohon birni ne a asalin babban birnin masarautar bayan da Daurama ta ɗauke shi daga garin ta mai da shi sabon birnin Daura, wanda aka sama garin sunanta.[1]