David Muir | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Syracuse (en) , 8 Nuwamba, 1973 (51 shekaru) |
ƙasa | Tarayyar Amurka |
Karatu | |
Makaranta |
Ithaca College (en) University of Salamanca (en) Georgetown University (en) Roy H. Park School of Communications (en) |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan jarida |
Employers | American Broadcasting Company |
IMDb | nm1586318 |
David Jason Muir (An haife shi ranar 8 ga watan Nuwamba, 1973). Ɗan jaridar Ba'amurke ne kuma mai gudaner da shiri ABC World News na dare kuma mai haɗin gwiwa ne na mujallar ABC News 20/20, wani ɓangare na sashen labarai na gidan talabijin na watsa labarai na ABC, wanda ke Birnin New York. Muir a baya ya yi aiki a matsayin mai gudanar da shiri karshen mako kuma bangare na farko a gidan Talabijin na ABC na Dare tare da Diane Sawyer, wanda ya gaje ta a ranar 1 ga watan Satumba, shekarar 2014. A ABC News, Muir ya lashe lambar yabo Emmy da Edward R. Murrow da yawa saboda aikin jarida da na duniya.
Dangane da Rahoton Tyndall, rahoton Muir ya sami mafi yawan loka shekarar in iska a cikin shekarar 2012 da shekara ta 2013, wanda ya sa ya zama ɗayan fitattun 'yan jarida a Amurka. Labaran Duniya a Dare tare da David Muir ya zama gidan labarai da aka fi kallo a Amurka. A shekarar 2013, shirin telebijin na mako yazo na "12 da ake kalla a cikin Labaran Talabijin". Muir da aka jera a matsayin daya daga cikin wonda ya fi daukan sha´awa a shekarar 2014.