Doka Akan Namun daji | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | Doka |
Facet of (en) | farauta |
Dokan ƙayyade kamun Naman daji wasu ƙa'idoji ne waɗanda ke tsara ƴancin farautar ko kama, kashe wasu nau'ikan kifaye da namun daji ( Namun daji ). [1]An ƙayyade wasu daga cikin waɗan su iyakoki akan namun daji, Abubuwan da aka ƙayyade su na iya haɗawa da abubuwa masu zuwa: Ƙayyade kwanakin kamun kifi ko nama zai iya amfani dashi a wani lokaci, taƙaita adadin dabbobin da kowane mutum zai iya kamawa, taƙaita nau'in mutun farauta, da iyakance makamai da kayan kamun kifi da ake amfani da su ko yin farauta.Mafarauta, masunta da ƴan mahukunta gaba ɗaya sun yarda cewa makasudin irin waɗannan dokokin shine a daidaita buƙatun kiyayewa da da kuma kamun da sarrafa yanayi da yawan kifi da namun daji. Dokokin za su iya ba da tsarin doka mai kyau don tattara kuɗin lasisi da sauran kuɗi waɗanda ake amfani da su don tallafawa ƙoƙarin kiyaye namun daji tare da samun bayanan kamun shi da aka yi amfani da su a aikin sarrafa namun daji.[2][3]