![]() | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Burkina Faso | |||
Region of Burkina Faso (en) ![]() | Sahel Region (en) ![]() | |||
Province of Burkina Faso (en) ![]() | Séno Province (en) ![]() | |||
Babban birnin |
| |||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 46,521 (2019) | |||
• Yawan mutane | 18.37 mazaunan/km² | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 2,532 km² |
Dori (wanda aka fi sani da Winde ko Wendu[1]) birni ne, da ke arewa maso gabashin Burkina Faso, kusa da iyakar ƙasar Nijar. Birnin na dai-dai kusa da 14°02′N 0°02′W / 14.03°N 0.03°W. Birnin ne babban birnin yankin Sahel, kuma yana da yawan jama'a 46,512 (a alkaluman 2019).[2] Babbar kabilar mazauna birnin ita ce Fula (Fulani) amma ƴan ƙabilar Abzinawa da Songhai galibi akwai su jefi-jefi. Gari ne da ya shahara da makiyaya da kuma shahararrun kasuwannin dabbobi.[3]
Yanayin zafin a Dori, ya kai kashi 47.2 °C (117.0 °F) ° C (117.0 ° F) a shekara ta 1984, wanda shine mafi girman yanayin zafi na ma'aunin selshiyos da aka taɓa samu a ƙasar Burkina Faso.[4]
A shekarar 2020, an ruwaito cewa Sarkin Liptako ya yi rayuwa a Dori.[5]