![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 5 Mayu 2002 (22 shekaru) |
ƙasa | Ivory Coast |
Sana'a | |
Sana'a |
tennis player (en) ![]() |
Tennis | |
Eliakim Coulibaly (an haife shi ranar 5 ga watan Mayu 2002) ɗan wasan tennis ne na Ivory Coast.
Coulibaly yana da babban matsayi na ATP guda 479 wanda aka samu a ranar 17 ga watan Oktoba 2022. Hakanan yana da babban matsayi na ATP mai ninki biyu na 613 da aka samu a ranar 3 ga watan Oktoba 2022.[1]
Coulibaly ya kuma buga wasa a matakin yara kanana kuma ya kai matsayin babban matsayi na 16 a ranar 6 ga watan Janairu, 2020 kuma ya buga rikodin cin nasara na 85 – 36 a cikin guda da 45 – 34 a ninki biyu.[2]
Coulibaly yana wakiltar Ivory Coast a gasar cin kofin Davis, inda yake da rikodin W/L na 2-0.
Coulibaly ya fara atisayen wasan tennis a Abidjan kafin ya koma Casablanca yana dan shekara 12.[3] A halin yanzu yana zaune a kudancin Faransa kuma yana horo a Kwalejin Tennis ta Mouratoglou. [4] Coulibaly shi ne babban dan wasan Tennis na Afirka, yayin da shi da dan Afirka ta Kudu Khololwam Montsi suka zama 'yan wasan Afrika na farko da suka kai matsayi na 20 a jerin kananan yara na ITF. [5]