![]() | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Fadak (Larabci فدك) wani yanki ne na lambu a cikin Khaybar(خيبر), wani yanki a arewacin Arebia ; yanzu ta zama ƙasar Saudiyya . Ya kasance kusan 140 kilometres (87 mi) daga Madina, Fadak an san ta da rijiyoyin ruwa, dabino, da aiyukan hannu. [1] Lokacin da musulmai suka ci mutanen Khaibara a yaƙin Khaybar ; 'Fadak' yana daga cikin falalar da aka yiwa annabin musulunci Muhammad . An ce Fadak ya zama abin da wasu gungun Musulmi suka yi saɓani a tsakanin Fatimah da khalifa Abubakar bayan mutuwar Annabi Muhammad.[ana buƙatar hujja]