Filin jirgin saman Douala tare da jiragen sama a cikin layin jirgin Duba gaban filin jirgin saman Douala na duniya a rana mai haske
Filin jirgin sama na Doaula ya kasance filin jirgin sama ne na ƙasa da ƙasa dake a Douala a Kasar Cameroon, wanda shine mafi girma a birni kuma babban birnin ƙasar Kamaru. Filin jirgin saman Douala yana da titin jirgin sama guda ɗaya, 12/30, tare da tsayin 2,880 m (9,448 ft) Tsakanin ranar 1 da kuma ranar 21 ga watan Maris na shekara ta 2016, titin jirgin ya rufe don ayyukan haɓaka; duk kamfanonin jiragen sama sun sauya aiki zuwa Filin jirgin saman Yaoundé a wannan lokacin. [1] Wannan ya zama wani ɓangare na shirin gyara na biliyan 20 na CFA (36,363,636 dala miliyan), wanda Hukumar Raya Cigaban Faransa ta ba da kuɗin, wanda ke niyyar gyara matakai biyu: da farko hanyar saukar jirgin sama, sannan tashoshinta da ciki.