![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Onitsha, 26 ga Yuni, 1984 (40 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Karatu | |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a |
Paralympic athlete (en) ![]() |
Tsayi | 165 cm |
Kyaututtuka |
Flora Ugwunwa (an Haife ta a ranar 26 ga watan Yuni 1984) [1] 'yar wasan Paralympic ce ta Najeriya wacce ke fafatawa a cikin abubuwan da aka tsara na F54 . [2] Ta wakilci Najeriya a gasar wasannin nakasassu ta bazara na shekarar 2016 da aka gudanar a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil kuma ta lashe lambar zinare a gasar jefa mashin na mata (women's javelin thrower) na F54. [2] Ta kuma kafa sabon tarihin duniya na mita 20.25 a wannan taron. [3]
Ta wakilci Najeriya a gasar wasannin nakasassu ta bazara na shekarar 2020 a birnin Tokyo na kasar Japan bayan ta lashe lambar azurfa a gasar jefa mashin na mata F54 a gasar tseren guje-guje da tsalle-tsalle ta duniya na shekarar 2019 da aka gudanar a birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa.[4] Ta kuma fafata a gasar harbin mata (women's shot put) ta F54 inda ta kare a matsayi na 6.