Goronyo Dam | |
---|---|
![]() | |
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya |
Jihohin Najeriya | jihar Sokoto |
Ƙananan hukumumin a Nijeriya | Goronyo |
Coordinates | 13°31′50″N 5°52′56″E / 13.5306°N 5.8822°E |
![]() | |
Altitude (en) ![]() | 21 m, above sea level |
History and use | |
Opening | 1992 |
Maximum capacity (en) ![]() | 976 Dubu Dari |
Karatun Gine-gine | |
Tsawo | 21 m |
Tsawo | 12,500 meters |
|
Dam din Goronyo ya datse kogin Rima da ke Karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto a arewacin Najeriya. An kammala shi a cikin shekarar alif dari tara da tamanin da hudu 1984 kuma an ba da kwamishin din sa a shekarar alif dari tara da casa'in da biyu 1992. Dam din yana da tsari ne mai cike da yashi mai tsayin mita ashirin da daya 21 da tsayin jimlar 12.5 km. Yana da damar ajiya na 976 miliyan cubic mita.[1] Dam din zai kasance muhimmi wajen shawo kan ambaliyar ruwa da kuma fitar da ruwa a lokacin rani domin aikin da ake shirin yi na Zauro polder a jihar Kebbi.[2]
A watan Agustan shekarar dubu buyu da tara 2009, Gwamna Aliyu Magatakarda Wamakko ya bukaci Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta kammala aikin noman rani.[3] Shugaban marasa rinjaye na majalisar dokokin jihar Sokoto, Alhaji Bello Goronyo, ya ce ana bukatar Naira biliyan 4 don kammala aikin gyaran fuska, amma kusan Naira miliyan 600 ne aka bayar a kasafin kudin shekarar 2009.[4]