Hadiza Shagari | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | Abuja, 12 ga Augusta, 2021 |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Hausa |
Sana'a | |
Sana'a | First Lady (en) |
Hadiza Dawaiya Shagari, wacce aka fi sani da Hadiza Shehu Shagari (1940/41 – 12 Agustan 2021) ta kuma kasance jigo a Najeriya, tsohuwar uwargidan shugaban ƙasar Najeriya ce daga shekarar 1979 zuwa 1983, kuma matar Shehu Shagari.[1] Tare da kuma sauran matan Shehu Shagari guda biyu, Hadiza Shagari ta kasance uwargidan shugaban ƙasar Najeriya a lokacin da mijinta ya karɓi shugabancin ƙasar daga 1 ga Oktoban 1979 zuwa 31 ga Disambar 1983.[2][3]