Iri | aukuwa |
---|---|
Kwanan watan | 1 Oktoba 2010 |
Wuri | Abuja |
Adadin waɗanda suka rasu | 12 |
Adadin waɗanda suka samu raunuka | 17 |
Tashin bama-bamai na watan Oktoba a shekara ta 2010 a Abuja, Wanda ake kuma kira da tashin bama-bamai a ranar ƴancin kai na Najeriya a shekarar 2010 , wasu hare-haren bam ne da mota guda biyu da aka kai kan jama’ar da ke bikin cika shekaru hamsin da samun ‘yancin kai a babban birnin tarayya Abuja da safiyar ranar 1 ga watan Oktoba, shekara ta 2010. Hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane 12 tare da jikkata 17. A cewar majiyoyi da yawa,[1][2] ƙungiyar Movement for the Emancipation of the Niger Delta (MEND) ta yi gargadi ƙasa da sa'a guda kafin tashin bom na farko da ya fashe, kusa da dandalin Eagle Square (wuri na bikin), sai kuma, wajen ƙarfe 10:30 na safe, sauran bama-bamai suka tashi.[3]
Fashewar farko ta faru ne da misalin ƙarfe 10:30 na safe, jami'an agajin gaggawa sun isa wurin sannan kuma fashewa ta biyu ta afku biyo bayan fashewar bom na farko.[2]