Harshen Hausa | |
---|---|
Hausa | |
'Yan asalin magana | harshen asali: 43,900,000 (2019) |
Baƙaƙen boko da Baƙaƙen larabci | |
Lamban rijistar harshe | |
ISO 639-1 |
ha |
ISO 639-2 |
hau |
ISO 639-3 |
hau |
Glottolog |
haus1257 [1] |
Harshen Hausa, na ɗaya daga cikin rukunin Harsunan Chadic, kuma a ƙungiyar Harsunan Chadic kan, wanda ke cikin iyalin harshen Afroasia.
Harshen Hausa ɗaya ne daga cikin harsunan Najeriya. Shi ne yare mafii girma a ƙasar Najeriya. Masu magana da harshen Hausa a Najeriya sun kai kashi hamsin da biyar (55%) na al'ummar ƙasar.[2][3] Harshen Hausa yana yaďuwa ne ta hanyar ƴan-kasuwa. Wato yan kasuwan da suke tafiya daga ƙasar Hausa zuwa wasu ƙasashe da Nufin yin kasuwanci, hakan ya ƙara daukaka harshen.
Hausa da Hausawa a fadin duniya. Idan aka ce Hausa ana nufin duk wani abu da yake da alaƙa da Hausawa ko kuma ƙasashensu, da harshen su.[4] Hausawa nada asali a Kasar Najeriya da kasar Habasha wato (Ethiopia), wanda ya yaɗu a duk fadin duniya. Ana kuma kiran masu amfani da harshen da suna Hausawa, ƙasar Hausa tana da tarihi mai yawa, tun kafin zuwan Turawa da Larabarawa kasar Hausa, Hausawa suna da sarakuna da sutturu da sana'oi masu tarin yawa. Misalan sarakuna sarkin musulmi, sarkin Kano, Sarkin Zazzau, Sarkin Katsina, Sarkin Daura, Sarkin Gombe da sauran su. Misalan sutura babbar riga, kwado da linzami, yar shara da sauran su. Misalan sana’oi fawa, noma, kiwo, saka, farauta, kira da sauran su.
Akwai yardar cewa yaren Hausa ya samo asali ne daga Bayajidda wanda Balarabe ne, ya zo kasar Hausa a garin Daura domin kasuwanci.
Amma Kuma wannan magana ta tarihin Bayajidda akwai maganganu a kanta.