Hijira asalin kalmar Larabci ce da aka arota zuwa yaran Hausa, (ma'anar kalmar shine kaura daga wani guri zuwa wani guri,amman galibi domin samun salama) wanda kalmar zata dace da ita a hausa itace Kaura, amman ma'anan kalmar a addinin Musulunci na nufin:- "Hijiran da Manzon Allah yayi tare da Abubakar Siddiq daga Makkah zuwa Madinah (Yasrib) a shekarar (622) [1] bayan kafiran makkah sun tsara su kashe shi a watan Janairu shekara 622, sai Allah ya umurci Annabi da yayi Hijira daga Makkah zuwa Madinah,wanda a wancan lokacin ana kiran garin da Yasriba, zuwan Annabi garin keda da wuya, sai aka sama garin suna da Madina ma'ana Birni[2][3][4][5][6][7][8][9]
Hakan yasa Musulmai suka samu kalandar da ake kiran shi da suna Hijira kalanda[10][11][12][13][14][15]
Kafirai sunyi ittifaqi akan zasu kawo saurayi guda daya daga cikin kowace kabila ta larabawa tayanda idan Annabi ya fito daga gidanshi zasu yi masa dukan kwap daya gabadayansu domina jininshi ya watsu a cikin qabilun larabawa ta yanda makusantanshi baza su iya yaqan dukkan larabawa ba. <ref> Samfuri:Kulasatun nuril yaqin