![]() | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Najeriya, 31 Disamba 1923 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mutuwa | Najeriya, 14 Nuwamba, 2016 | ||
Karatu | |||
Makaranta | Kwalejin Barewa | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan kasuwa | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci |
Ibrahim Dasuki shine wanda ya kasan ce Sarkin Musulmi na 18, wanda aka hamɓarar a shekarar 1996 a lokacin gwamnatin soja ta Sani Abacha , Kafin ya zama Sarki. San nan ya riƙe sarautar Baraden jihar Sokoto. Dasuki shine Sarki na farko daga layin Buhari na gidan Dan Fodiyo . Ya kasance babban aminin Ahmadu Bello, aminin Abubakar Gumi kuma yana da tasiri a kafuwar Jama'atu Nasril Islam.