An taskan ce wannan muƙalar a cikin jerin Muƙaloli_masu_kyau a Hausa Wikipedia
Ana sa ran wata rana wannan muƙalar zata kasance a Babban Shafin Muƙalar mu a yau |
Ibrahim Shema | |||
---|---|---|---|
29 Mayu 2007 - 29 Mayu 2015 ← Umaru Musa Yar'Adua - Aminu Bello Masari → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Dass (Nijeriya), 22 Satumba 1952 (72 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Hausa | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello | ||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Barista Ibrahim Shehu Shema (an haife shi ranar 22 ga watan Satumba, shekarata 1957) lauya ne kuma ɗan siyasa ɗan Najeriya wanda aka zaɓe shi gwamnan jihar Katsina da ke a arewa maso yammacin ƙasar a lokacin babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2007.[1]
An sake zaɓen shi na tsawon shekaru huɗu a ranar 28 ga watan Afrilu, shekarar 2011, ya yi dukkan takarar a ƙarƙashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).[2] Wa’adinsa na biyu a kan ƙaragar mulkin gwamnan jihar na shekaru huɗu ya ƙare ne, a ranar 29 ga watan Mayun shekara ta 2015, daga nan ya mikawa Aminu Bello Masari zaɓaɓɓen gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress Mulki biyo bayan sabon babban zaɓen ƙasar na shekarata2015.