![]() | |||
---|---|---|---|
| |||
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 15 century | ||
ƙasa | Masarautar Benin | ||
Mutuwa | unknown value | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama | Ozolua | ||
Yara |
view
| ||
Sana'a | |||
Sana'a |
ɗan siyasa, dowager (en) ![]() |
Sarauniya Idia ita ce mahaifiyar Esigie, Oba (sarkin) Benin, wanda ya yi sarauta daga 1504 zuwa 1550. Ta taka muhimmiyar rawa a wajen tasowa da kuma mulkin ɗanta, ana ɗaukarta a matsayin babbar jaruma wacce ta yi yaƙi dare da rana, kafin da kuma lokacin sarautar ɗanta a matsayin oba ( sarki ) na mutanen Edo.[1] Sarauniya Idia taka rawar gani a wajen tabbatar da taken oba ga Esigie bayan mutuwar mahaifinsa Oba Ozolua. A dalilin haka, ta hada rundumar sojoji don su yaƙi ɗan'uwansa Arhuaran, wanda daga baya aka ci shi da yaƙi. Ta haka ne Esigie ya zama Sarki na 17 na Benin.[2] [3]
Esigie ne ya kafa taken iyoba (uwa sarauniya) kuma ya baiwa mahaifiyarsa, tare da Eguae-Iyoba (Fadar Uwa Sarauniya). [4]