Jacob Maliekal (an haife shi a ranar 1 ga watan Janairu shekara ta alif dari tara da casa'in da daya miladiyya 1991) dan wasan badminton ne na Afirka ta Kudu.[1] Ya zama dan wasan badminton na Afirka ta Kudu a shekarar ta 2009 kuma ya lashe lambobin zinare a gasar cin kofin Afirka ta shekarun 2011 da 2014 a gasar maza ta badminton.[2] Ya fafata ne a gasar Olympics ta bazara ta shekarar 2016 da aka gudanar a Rio de Janeiro, Brazil.[3]
Ya kasance daya daga cikin 'yan wasa 14 da aka zaba don shirin Road to Rio, shirin da ke da nufin taimakawa 'yan wasan badminton na Afirka su shiga gasar Olympics ta lokacin zafi na 2016.