![]() | ||||
---|---|---|---|---|
جدة (ar) | ||||
| ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Saudi Arebiya | |||
Province of Saudi Arabia (en) ![]() | yankin Makka | |||
Governorate of Saudi Arabia (en) ![]() | Jeddah Governorate (en) ![]() | |||
Babban birnin |
Jeddah Governorate (en) ![]() | |||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 4,697,000 (2021) | |||
• Yawan mutane | 860.26 mazaunan/km² | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 5,460 km² | |||
Wuri a ina ko kusa da wace teku | Red Sea | |||
Altitude (en) ![]() | 12 m-7 m | |||
Tsarin Siyasa | ||||
• Gwamna |
Saleh Al-Turki (en) ![]() | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Lambar aika saƙo | 21000 | |||
Kasancewa a yanki na lokaci |
UTC+03:00 (en) ![]() | |||
Tsarin lamba ta kiran tarho | 12 |
Jeddah ko Jiddah ko kuma Jedda; da larabci|جدة, Birni ne dake Tihamah a yankin Hejaz dake gabar Kogin Maliya kuma shine babban birni a yammacin kasar Saudiya. Itace mafi yawan al'ummah a Makkah Province [1], kuma itace keda babban tashar Ruwa a kogin Maliya, tanada adadin mutane kusan miliyan hudu (4,000,000,) tun a kidayar a shekara ta 2017. Kuma itace gari na biyu mafiya yawan al'ummah a kasar Saudiya bayan birnin Riyadh. Jeddah itace cibiyar kasuwancin kasar Saudiya.[2]
Jeddah ce mashigar garin Mecca da Medina, garuruwa biyu masu tsarki a addinin musulunci, kuma garuruwan yawon bude ido.
Dangane da tattalin arziki, Jeddah tana fuskantar Karin cigaba wurin sanya jari a abubuwan dasuka shafi kimiyya da kyerekyere dan tazamo kangaba a kasar ta Saudiya dama yankin gabas ta tsakiya.[3] ansanya Jeddah na hudu a biranen kasar Afirka da Gabas ta tsakiya masu kirkire kirkira a shekara ta 2009 a jerin sunayen birane dake kirkiran sabbin abubuwa.[4]
Jeddah nadaya daga cikin biranan shakatawa a kasar Saudiya kuma ansanyata a cikin kasashe masu kyawu, daga cibiyar nan na Globalization and World Cities Study Group and Network (GaWC). Kasantuwar garin a gabar teku yasa mafi yawan abincinsu yazama kayayyakin ruwa ne, da al'adar da kuma kamun kifi, wanda bazaka ga hakan asauran garuruwan Saudiya ba. Da larabci taken birnin itace "Jeddah Ghair," fassara wato "Jeddah daban ce." Hakane yasa taken mafiya yawan al'ummah garin da yanwaje suke amfani dashi. Ana ganin birnin Jeddah a matsayin garin dayafi tarbar kowa da kowa a kasar Saudiya.