Jon Seda | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | New York, 14 Oktoba 1970 (54 shekaru) |
ƙasa | Tarayyar Amurka |
Mazauni | Chicago |
Harshen uwa | Turanci |
Karatu | |
Makaranta | Clifton High School (en) |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi, ɗan wasan kwaikwayo, dan wasan kwaikwayon talabijin da boxer (en) |
IMDb | nm0781218 |
Jonathan Seda (an haife shi ne a ranar 14 ga watan Oktoba, a shekarata 1970). ɗan wasan kwaikwayo ne Ba'amurke. Kuma ɗan dambe ne mai son bita wanda ya taka rawa a matsayin Gladiator a wani fim ɗin dambe wanda kuma aka yi a shekarar 1992.
Ya taka rawar Chris Pérez tare da Jennifer Lopez a cikin fim ɗin Selena da kuma jami'in tsaro Antonio Dawson a NBC na Chicago PD. Ya kuma taka rawar Paul Falsone a cikin wasan Homicide: Life on the Street . Ya kuma taka rawar US Marine John Basilone, mai kambar lambar girmamawa a Tom Hanks da Steven Spielberg ya bisa zuwa Band of Brothers, The Pacific.