journalism | |
---|---|
industry (en) , academic discipline (en) da genre (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | aiki |
Product, material, or service produced or provided (en) | labarai, Bayani da labari |
Has characteristic (en) | journalism genre (en) |
Tarihin maudu'i | history of journalism (en) |
Gudanarwan | ɗan jarida, newsmaker (en) da fixer (en) |
Aikin jarida shine samarwa da rarraba rahotanni game da hulɗar abubuwan da suka faru na waje daban daban, gaskiya, ra'ayoyi, da mutanen da suke " labaran ranar" da ke sanar da al'umma zuwa akalla wani mataki na daidaito. Kalmar, suna, ta shafi sana'a (Professional or not), hanyoyin tattara bayanai, da kuma tsara salon adabi. Kafofin watsa labaru sun haɗa da print, talabijin, rediyo, Intanet, da kuma, a baya, newsreels.
Matsayin da ya dace na aikin jarida ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa, kamar yadda ma'anar sana'ar take, da matsayin da aka samu. A wasu ƙasashe, gwamnati ce ke kula da kafafen yada labarai kuma ba sa cin gashin kansu. [1] A wasu kuma, kafofin watsa labarai masu zaman kansu ne daga gwamnati kuma suna aiki azaman masana'antu masu zaman kansu. Bugu da kari, kasashe na iya aiwatar da dokoki daban-daban da suka shafi 'yancin fadin albarkacin baki, 'yancin 'yan jaridu da kuma maganganun batanci da libel cases.
Yaduwar Intanet da wayoyin hannu ya kawo gagarumin sauyi a fagen yada labarai tun farkon karni na 21. Wannan ya haifar da sauyi a cikin amfani da tashoshi na jaridu, yayin da mutane ke ƙara jin labarai ta hanyar masu karantawa ta e-reading, wayoyin hannu, da sauran na'urorin electronic device, sabanin yadda aka saba da tsarin jaridu, mujallu, ko tashoshi na talabijin. Ana ƙalubalantar ƙungiyoyin labarai da su sami cikakken kuɗin shiga reshe na dijital, da kuma inganta yanayin da suke bugawa a cikin bugawa. Jaridu sun ga kudaden shiga na bugawa suna nutsewa cikin sauri fiye da adadin girma na kudaden shiga na dijital.