Katsina, mai yiwuwa kalmar daga "Tamashek" (yana nufin ɗa ko jini) ko mazza (maza) tare da "inna" (uwa). Karamar hukuma ce kuma babban birnin Jihar Katsina, Arewacin Najeriya. Katsina tana da nisan kilomita 260 km (160 mil) daga gabashin Birnin Sokoto, da kuma kilomita 135 Km (84 mil) daga Arewa Maso Yammacin Birnin Kano, tana kusa da iyakar ƙasar Nijar.
An ƙiyasta yawan mutanen Dake cikin Birnin Katsina a shekare ta 2016 da kimanin mutum 429,000.[1]
Birnin ya kasance cibiyar noma da kiwo inda ake noman gyaɗa da auduga da fatu da gero da kuma dawa,[2] sannan har ila yau, akwai masana'antun sarrafa man-gyaɗa, da ƙarafa, sannan birnin ya kasance cibiyar kiwon dabbobi kamar su shanu, tumakai, awakai da kaji da sauransu
Mafi akasarin mutanen birnin Musulmai ne daga ƙabilar Hausa da Fulani.
Tsohon shugaban kasan Najeriya Umaru Musa Yar'Adua ya kasance babban mutum ne daga Katsina.[3]
Gwamna mai ci na yanzu a Jihar Katsina shi ne Aminu Bello Masari,[4] wanda aka rantsar a matsayin gwamnan jihar a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2015, wanda ya gaji kujerar daga hannun Bar. Ibrahim Shema.[5]