Katsina : Mai yiwuwa kalmar daga "Tamashek" (yana nufin ɗa ko jini) ko mazza (maza) tare da "inna" (uwa). Karamar hukuma ce kuma babban birnin Jihar Katsina, Arewacin Najeriya. Katsina tana da nisan kilomita 260 km (160 mil) daga gabashin Birnin Sokoto, da kuma kilomita 135 Km (84 mil) daga Arewa Maso Yammacin Birnin Kano, tana kusa da iyakar ƙasar Nijar.
An ƙiyasta yawan mutanen Dake cikin Birnin Katsina a shekare ta 2016 da kimanin mutum 429,000.[1] Birnin akasarin mutanen birnin Musulmai ne daga ƙabilar Hausa da Fulani.
Tsohon shugaban kasan Najeriya Umaru Musa Yar'Adua ya kasance babban mutum ne daga Katsina.[2]
Gwamna mai ci na yanzu a Jihar Katsina shine
Umar dikko radda,[3] wanda aka rantsar a matsayin gwamn.an jihar aranar29 ga watan mayu
Shekara ta 2023
, wanda ya gaji kujerar daga hannun Bello Aminu Masari.[4]