Jihar Kebbi jiha ce dake a kasar Najeriya. Tana da yawan fadin kasa kimanin kilomita murabba’i 36,800 da yawan jama’a milyan uku da dubu dari shida da talatin da dari takwas da talatin da daya (jimillar 2005). An samar da jihar Kebbi ne daga Jihar Sakkwato a ranar 27 ga Agustan shekarar 1991 a lokacin mulkin Janar Ibrahim Babangida. Babban Birnin Jihar shi ne Birnin Kebbi. Jihar Kebbi ta kasu zuwa kananan hukumomi 21, da masarautu hudu (Gwandu, Argungu, Yauri da Zuru), da gundumomi 35. Jihar Kebbi ta samo sunan ta ne daga karni na 14" MULKIN KEBBI" wanda ya kasance lardin tsohuwar daular Songhai. Musulunci shine addini mafi rinjaye.
Jihar tana Arewa maso yammacin Najeriya, jihar Kebbi tana da fadin murabba'in kilomita 36,800. Jihar Kebbi tana da iyaka da jihar Sokoto a bangaren arewa maso gabas, jihar Zamfara daga gabas, jihar Neja ta bangaren yamma sannan kudu da jamhuriyar Nijar a bangaren yamma.