Kudancin Afirka

Kudancin Afirka


Wuri
Map
 25°52′45″S 23°05′51″E / 25.879106°S 23.097578°E / -25.879106; 23.097578
Yawan mutane
Faɗi 69,235,159 (2023)
Labarin ƙasa
Bangare na Afirka
Sun raba iyaka da
Wannan Muƙalar guntuwa ce: tana buƙatar a inganta ta, kuna iya gyara ta.

Kudancin Afirka shi ne yankin kudu maso yammacin Afirka. Babu ma'ana daya da aka amince da ita, sune wasu gungun kasashe kamar su da geoscheme na Majalisar Dinkin Duniya, Kungiyar Cigaban Afirka ta Kudu ta gwamnatocin Afirka, da yanayin muhalli dangane da halayen kasar.

Kamar yadda kimiyyar yanayi na zahiri ta bayyana ta, Kudancin Afirka gida ne ga yawancin yankuna ruwa; kogin Zambezi ne ya fi fice. Zambezi yana gudana daga kusurwar arewa maso yammacin Zambia da yammacin Angola zuwa Tekun Indiya a gabar tekun Mozambik. A kan hanyarta, tana gudana a kan babban rafin Victoria da ke kan iyakar Zambia da Zimbabwe. Victoria Falls na daya daga cikin manyan magudanan ruwa a duniya kuma babban wurin yawon bude ido a yankin.[1]

Kudancin Afirka ya hada yanayi mai zafi da yanayi mai sanyi, tare da Tropic of Capricorn ya wuce har zuwa tsakiyar yankin, ya kuma rarraba yankin zuwa wurare masu zafi da wurare masu sanyi. Kasashen da aka fi la'akari dasu a matsayin Kudancin Afirka sun hada da Angola, Botswana, Comoros, Eswatini, Lesotho, Madagascar, Malawi, Mauritius, Mozambique, Namibia, Afirka ta Kudu, Zambia, da Zimbabwe. A cikin tarihin gargajiya, ba'a cika sanya tsibirin Madagascar acikin yankin ba saboda bambancin yare da al'adunsu.[1]

Majalisar Dinkin Duniya geoscheme ga Afirka 
  1. 1.0 1.1 "Southern Africa".

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Nelliwinne