Kungiyar Kwallon Kwando ta Maza ta Aljeriya | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | national basketball team (en) |
Ƙasa | Aljeriya |
Ƙungiyar kwallon kwando ta Aljeriya ɓangaren kwallon kwando na maza ne dake wakiltar Algeria a gasar ƙasa da kasa, wanda hukumar kula da wasan kwallon kwando ta Algérienne de Basket-Ball ke gudanarwa. [1]
Tawagar ta dai ta kare ne a zagaye na hudu na ƙarshe a duk lokacin da ta karɓi bakuncin manyan gasar kwallon kwando ta ƙasa da ƙasa da suka hada da gasar kwallon kwando ta Afirka da kuma wasannin Afirka baki ɗaya . Sun buga gasar cin kofin duniya ta FIBA a shekarar 2002 a Amurka inda suka kare a mataki na 15.