Legas islandJihar lagos mai yawan jama'achunkoson jama'a a garin LagosBene na farko a Nigeria wanda ke birnin Badagry a LagosBabban filin jirgin sama dake Tinubu Square Lagos wanda aka fi sani da "Murtala Muhammad International Airport"Gabar Teku na Badagry wanda ke babban birnin LagosBabbab Asibitin EKO dake Victoria Island a LagosTinubu Square
Birnin Legas, ko kuma Birnin Ikko, shi ne babban birnin jahar Legas da ke Najeriya. Legas tana daya daga cikin birane mafi girma da yawan jama'a a Afirka da ma duniya baki daya. Legas ne birni na biyu mafi girma a Afirka, kuma na bakwai a duniya.[1] Kimanin mutum miliyan 15.3 (a shekara ta 2022) ke rayuwa a Legas.[2] Garin Legas na da mutane kimanin 23.5 million a shekara ta 2018, wanda ya maida shi babban birni mafi girma a nahiyar Afirka. Legas ta kasance cibiyar kasuwanci a jahar Legas da Najeriya gaba daya.[3][4]
Legas tana daya daga cikin birane goma masu habbaka da sauri a duniya[5][6]Babban birnin yana matsayin na hudu a kawo kudin shiga (GDP) a Africa[7]kuma akwai daya daga cikin tashar jiragen ruwa mafi hada-hada Afirka.[8]Birnin Legas cibiya ce ta ilimin gargajiya a sassan Afirka da ke kudancin sahara.
Legas ada gida ne ga mutanen Awori, wani reshe ne na Yarbanci na yammacin Afirka. Amma yanzu ta zama birnin tashoshin jiragen ruwa wanda ya samo asali daga tsibirai daban,daban.[9]
Gwamnatin tarayya ke gudanar da harkokin wannan babban birni har izuwa shekarar 1967 lokacin da aka rarraba birnin zuwa kananan hukumomi 7 da muke dasu a yau.[10][11] da kuma karin birane 3 wanda yasa kananan hukumomin suka koma 13 wanda suka samar da jahar Legas na yau.[12][13]
Har wa yau, an mai da Ikeja ta zamo babban birnin jahar a shekara ta (1976), sannan Abuja ta koma babban birnin tarayya a shekara ta (1991). Wuraren da ake kira birnin Legas watau "Lagos Metroplitan Area"[14][15][16]sun hada da manyan biranen[17] jahar guda 16 har da Ikeja. Wannan manyan birane sun mamaye kashi 37% na fadin kasar Legas, sannan tana dauke da fiye da kaso 86% na mutanen jahar Legas.
Akwai rudani game da ainihin yawan mutane birnin Legas. A kidaya da akayi na shekara ta 2006 ya nuna cewa akwai adadin mutane miliyan 8 a birnin. Sai dai gwamnatin jahar ta nuna rashin amincewarta ga adadin kidayan inda ta daki nata adadin da kimanin mutane miliyan 16. A shekara ta 2015 wani kundi wanda gwamnati bata tantance shi ya sanya mutanen Legas har zuwa kusa da jahar Ogun kimanin mutum miliyan 21.[18][19][20]
↑A Flood-Free Lagos: The Regional Imperative". Retrieved 27 November2015.
↑"Olukoju, Ayodeji (1996). "The Travails of Migrant and Wage Labour in the Lagos Metropolitan Area in the Inter-War Years". Labour History Review. Liverpool University Press. 61: 49–70. doi:10.3828/lhr.61.1.49. Retrieved 27 November 2015.
↑"Lagos Metropolitan Area: Scope and scale of the shelter problem". Retrieved 27 November 2015.
↑"Administrative Levels - Lagos State". Nigeria Congress. Archived from the original on 25 December 2005. Retrieved 27 November 2015.
↑Metro Lagos (Nigeria): Local Government Areas". City Population. 21 March 2015. Retrieved 26 October 2015.
↑"Population". Lagos State Government. 2011. Archived from the original on 18 October 2015. Retrieved 3 November 2012.