Lei Jun (an haife shi a ranar 16 ga watan Disamba, 1969) ɗan kasuwa ne kuma mai ba da agaji. An san shi da kafa kamfanin waya na Xiaomi. Ya zuwa watan Oktoba na shekara ta 2022, an kiyasta darajar kuɗin Lei a ko dai dala biliyan 8.1 bisa ga Bloomberg Billionaires Index, wanda ya sanya shi mutum na 203 mafi arziki a duniya,[1] ko kuma a dala biliyan 7.5 da mujallar Forbes, ta ambata shi a matsayi na 265 a duk duniya.[2]