Mactabene Amachree (an haife ta ranar 30 ga watan Janairun, 1978) a Port Harcourt. tsohuwar ƴar wasan ƙwallon Kwando ce a Nijeriya. A shekarar 2001, ta zama ‘yar Najeriya ta farko da ta fara wasa a gasar WNBA.[1] Amachree ta taka leda a ƙungiyar ƙwallon Kwando ta mata ta ƙasa a gasar Olympics ta bazara ta 2004.[2] Ita kuma gimbiya ta dangin Ojuka na mutanen Kalabari a Najeriya.
- ↑ WNBA Player Bio Archived 2009-03-19 at the Wayback Machine
- ↑ (28 July 2005), Nigerian Finds Home in Washington, DC Women's Pro Basketball Team Archived 2009-03-19 at the Wayback Machine, VOA News. Retrieved 03-06-2009