![]() | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | cibiya ta koyarwa |
Ƙasa | Birtaniya |
Mulki | |
Hedkwata | Leicester |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1975 |
le.ac.uk… |
Makarantar Likitanci ta Leicester makarantar likitanci ce, wacce take a cikin Jami'ar Leicester. An kafa makarantar a shekarar 1975[ana buƙatar hujja], ko da yake tsakanin shekarar 2000 da 2007 ya kasance wani ɓangare na haɗin gwuiwar Makarantar Likita ta Leicester-Warwick. Tun daga 2010, makarantar likitanci ta yarda da ɗaliban Burtaniya 175 a kowace shekara sun haɗa da ɗalibai 20 daga ƙasashen waje.[1] Leicester ta kasance ta biyar (5th) a cikin Burtaniya, a tsakanin makarantun likitanci na 33 a cikin shekarata 2020 Shanghai na Jami'o'in Duniya. A cikin wannan martaba, Leicester ta kasance ta 20 a duniya. Makarantar Likita ta Leicester ita ce makarantar likitancin Ingila ta farko da ta fara aiwatar da shirin iPad-kowane-dalibi a matakin karatun, wanda ya fara a shekarar 2013.[2] Makarantar Likita ta Leicester tana ɗaya daga cikin makarantun likitancin Burtaniya waɗanda ke ba da rarraba jiki a matsayin ɓangare na koyarwar da harkokin lafiya.[3]