![]() | |||
---|---|---|---|
2022 - | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | jahar Legas da Najeriya, 20 century | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar Oxford Johns Hopkins Bloomberg School of Public Health (en) ![]() Jami'ar jahar Lagos | ||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a |
ɗan siyasa, dentist (en) ![]() |
Mariam Temitope Masha ita ce babbar mataimakiya ta musamman ga shugaban tarayyar Najeriya kan ayyukan jin kai. Kafin wannan nadin, ta yi aiki a matsayin babbar mataimakiya ta musamman ga shugaban Najeriya kan ‘Yan Gudun Hijira.[1] Ta kuma yi aiki a matsayin mai ba da shawara na musamman ga Mataimakin Shugaban kasa kan ayyukan Arewa maso Gabas. Memba ce a cikin kwamitin amintattu na mutum biyar tallafawa yaran yankin Arewa maso Gabas wato,North East Children's Trust (NECT), inda tayi aiki a matsayin sakatariyar zartarwa,[2] kuma ta kasance malama mai ziyartar African Leadership Center (ALC) na King's College London.[3]