![]() | |||
---|---|---|---|
27 ga Augusta, 1985 - 26 ga Augusta, 1993 ← Hadiza Shagari - Margaret Shonekan → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Asaba, 1 Nuwamba, 1948 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Hausa | ||
Mutuwa | Los Angeles, 27 Disamba 2009 | ||
Yanayin mutuwa | Sababi na ainihi (Ciwon Daji Na Ovarian) | ||
Ƴan uwa | |||
Abokiyar zama | Ibrahim Babangida | ||
Karatu | |||
Makaranta |
La Salle Extension University (en) ![]() | ||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa |
Maryam Babangida (An haife ta ne a ranar daya ga watan Nuwamba, shekara ta alif dari tara da arba'in da takwas miladiyya (1948), ta mutu a ranar ashirin da bakwai(27) ga watan Disambar shekara ta 2009 ta kasance uwargidan Janar Ibrahim Badamasi Babangida, wanda ya kasance shugaban kasar Nijeriya na mulkin soja daga shekara ta 1985 zuwa shekara ta 1993. An kuma zargi zamanin mulkin mijin nata da yawaitar cin hanci da rashawa. [1] A na tuna ta ne bisa kasancewarta wadda ta kirkiro mukamin ofishin d Shugaban Najeriya tare da nada kanta a matsayin wadda ta fara rike wannan mukami. A matsayinta na matar shugaban kasa, ta ɓullo da shirye-shirye da yawa domin inganta rayuwar mata. Hakan yasa ta zama sananniya kuma abar koyi a matsayin da ta rike bayan sauke mijinta daga mulki.