![]() | |
---|---|
| |
Rayuwa | |
Haihuwa | Kpalimé, 19 ga Faburairu, 1994 (31 shekaru) |
ƙasa | Togo |
Karatu | |
Makaranta |
Savoy Mont Blanc University (en) ![]() Emlyon Business School (en) ![]() |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a |
sportsperson (en) ![]() ![]() |
Mahalarcin
| |
Nauyi | 60 kg |
Tsayi | 163 cm |
Mamba |
emlyon alumni (mul) ![]() |
Mathilde-Amivi Petitjean (An haife ta a watan Fabrairu 19, 1994 [1] [2] ) 'yar wasan gudun kankara ce ta zagayen ƙasa 'yar ƙasar Faransa da Togo. Ta yi wa kasar Togo wasa a gasar Olympics na lokacin sanyi a shekara ta 2014 a tseren gargajiya na kilomita 10.[3] Petitjean ta kare a matsayi na 68 a tserenta guda daya tilo da ta yi a tsakanin 'yan wasa 75, kusan mintuna goma a bayan wacce tazo na daya wato Justyna Kowalczyk ta Poland. Petitjean na fatan cewa bayyanarta zai taimaka wajen zaburar da matasan Afirka don shiga cikin wasanni na hunturu.[4]
An haifi Petitjean a Togo, ga mahaifiya 'yar Togo wanda hakan ya ba ta damar yi wa kasar wasa. Kungiyar Ski ta Togo ta tuntube ta a cikin watan Maris 2013 ta kafar Facebook don yi wa kasar wasa a gasar Olympics na lokacin sanyi. Petitjean ta kwashe mafi yawan rayuwarta a Haute-Savoie, Faransa, inda ta koyi wasan tsaren kankara.[5]
Ta dauki tutar Togo a wajen bikin bude taron.[6]
Ta yi wa kasar Faransa wasa har zuwa lokacin da ta canza sheka zuwa Togo.